Saadou Bori – Bori Lyrics

Kai Bori ya koma ga yara
Kai Bori ya koma ga yara
Ya bar manyan mutane
Yara kanana masu Bori
Auta jan maye suka tsoro
Kai maye dan mayya suka tsoro
In iya ta kama yaka ceto
Auta ya kama ba a ceto

Kai mace kucaka bata Bori
Kai mace kazama bata Bori
Kai wani kyawo sai ga Bori
Kai wasu kaya sai ga Bori
Iya Bori abin haw tsoro
Aljani abun haw tsoro

Auta jan maye nika tsoro
Kai maye dan mayya nika tsoro
Haba! Maye

Kai Bori manyan sarakai
Yara kanana basu yi ne
Ali abokina na da Bori
Kai Jallo abokina na da Bori
Manu abokina na da Bori
Ni nasa kaina a Bori

Auta jan maye nika tsoro
Kai maye dan mayya nika tsoro
Haba maye!

Yan Borin gida da Borin daji
Bori ko gida shina iske doli

Ina mutuwa maza da tsoron soja?
Mutuwa ko gida tana iske kato

Na ce, "Soja birgimar hankaka"
Soja wuta gudu barewar daji

Ni na ce, "Hattara kumando mugu"
Shillo bashi kada dan jemage

Dan Allah maza kudauki sarushe
Mutuwa ko gida tana ishe kato

Wani ya sha wuta kamar bai sha ba
Wani yasha wuta jiki ya sale

Comments (0)